Isa ga babban shafi
Austria

An jinkirta sakamakon zaben Austria

Rahotanni daga kasar Austria na nuna cewa, ‘yan takarar shugabancin kasar guda biyu, Nobert Hofer da abokin hamayyarsa Alexander Van der Bellen sun yi kai-da-kai wajen samun yawan kuri’un da aka kada a zagaye na biyu na zaben da aka gudunar a yau Lahadi.

An dai zaton Nobert Hofer zai lashe zaben
An dai zaton Nobert Hofer zai lashe zaben REUTERS/Heinz-Peter Bader
Talla

Sakamakon karshe da zai nuna wanda ya yi nasara, ya ta’allaka ne a kan kammala kidiyar kuri’un da aka kada ta hanyar gidan waya, abinda ake ganin zai kai zuwa gobe Litinin kafin a kammala kidiyar.

Nobert Hofer na jam’iyyar Freedom Party mai ra’ayin rikau da Van der Bellen da ke samun goyon bayan ‘yan gwagwarmayar kare muhalli duk sun ce, nan da gobe ne za a san wanda ya yi nasara a cikinsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.