Kamfanin kera jiragen ruwan STX ya zama mallakin kasa
Faransa za ta mayar da kasaitaccen kamfanin kera jiragen ruwa ya zama mallakin kasar Faransa sakamakon takaddama da ta kaure tsakanin kasar da Italia wadanda ke kula da shi a matsayin hadin-gwiwa.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Faransa na bukatar a yi raba-daidai ne tsakaninta da wannan kamfani amma kuma Italia na nuna hakan ba mai yiwuwa ba ne.
Ministan tattalin arziki na Faransa Bruno Le Maire ne ya sanar da kwace harkokin kamfanin kera jiragen ruwan mallakin wani kamfanin Fincantieri na Italia, amma matakin zai kasance na dan wani lokaci ne har sai an sasanta.
Shi wannan kamfani STX da ke Saint-Nazaire, shi ne ya kera jiragen ruwa masu tarin yawa da suka hada da na yawon shakatawa da kuma na yaki, yana da gwanayen aikin na musamman, wadanda in ji ministan ba zai yiwu wata kasa ta kwace su ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu