rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ma’aikacin jinya ya kashe majinyata 90 a Jamus

media
A watan Fabrairun 2015 aka daure Hoegel Reuters

Rundunar ‘yan sandan Jamus, ta bankado cewa adadin mutane kusan 90 ne wani ma’aikacin jinya ya kashe wanda aka yankewa hukuncin daurin rai da rai, shekaru biyu da suka gabata, bisa laifin kashe wasu majinyata biyu, ta hanyar ba su magani fiye da kima.


Rahoton binciken da ‘yan sandan suka fitar, ya kara da cewa mai yiwuwa ne yawan wadanda ma’aikacin mai suna Niels Hoegel kashe su ya zarta 150.

A watan Fabrairun 2015 ne, Hoegel ya fara zaman hukuncin daurin rai da rai a gidan yari, bayan samunsa da kotu ta yi da laifin yi wa wasu marasa lafiya biyu da yake kula da su kisan gilla, da kuma yunkurin hallaka wasu majinyatan guda hudu da ke cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai, a asibitin Delmenhorst da ke arewacin garin Bremen.

Yanzu rundunar ‘yan sandan Jamus ta ce sakamakon binciken da ta jagoranta, ya bankado cewa ma’aikacin na da hannu wajen mutuwar akalla marasa lafiya 130 a asibitoci biyu da ya yi aiki, daga shekarar 1999 zuwa ta 2005, wanda aka danganta a matsayin daya daga cikin mafi munin kisan gillar da aka taba gani a Jamus.

‘Yan sandan na Jamus sun ce akwai hujjojin da suka tabbatar da kisan majinyata 90 da ma’aikacin jinyar mai shekaru 40 ya yi.

Tuni dai Hoegel ya amince da zargin da ake masa, tare da tabbatar da cewa yana yi wa marasa lafiyar da ya ke lura da su ne allurar magunguna masu karfin gaske da suke tsayar da aikin zuciyar dan adam, daga bisani kuma ya yi kokarin farfado da su.

A cewarsa yana yin hakan ne domin idan ya samu nasarar farfado da majinyatan ya kafa tarihi.

An tono gawarwakin mutane 130 domin gudanar da bincike, kuma sakamakon binciken ya tabbatar da sun mutu ne ta sanadin wasu manyan kwayoyi da ke kisa.