Mexico: Girgizar kasa ta hallaka sama da mutane 200
Girgizar kasa mai karfin gaske da ta aukawa tsakiyar kasar Mexico, tayi sanadin mutuwar sama da mutane 200, tare da rusa daruruwan gidaje.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Enrique Peña Nieto, ya ce sama da kanan yara 20 suka rasa rayukansu, yayinda wasu 30 suka bace bayanda makarantarsu ta rubza.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.1 da ta jijjiga makwabtan ihohin Mexico City, ta auku ne jim kadan bayan daruruwan ‘yan kasar ta Mexico, sun kammala karbar horon ceto da kuma bada agajin gaggawa a duk lokacin da aka samu girgizar kasa.
Ko a farkon watan Satumba, sai da wata girgizar kasar mai karfin maki 8.1 da ta aukawa kudancin kasar ta hallaka mutane 90.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu