rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
  • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
  • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.

Faransa Amurka Paris Barack Obama Francois Hollande

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsaffin shugabannin Faransa da Amurka sun gana kan yarjejeniyar yanayi

media
Barrack Obama ya yi fatar ganin Amurka ta koma cikin yarjejeniyar yanayi ta Paris don gogayya da sauran kasashen duniya. REUTERS/Kamil Krzaczynski

Tsohon shugaban kasar Amurka Barrack Obama da takwaransa na Faransa Francois Hollande sun yi wata ganawa a yau Asabar, inda suka tattauna kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris da kasashen duniya suka sanyawa hannu.


Tsaffin shugabnnin biyu sun yi imanin cewa, Yarjejeniyar ta zama tamkar guguwar da babu wanda zai iya tsayar da ita.

Obama wanda ke ziyara a birnin Paris na Faransa sun tattauna ne tare da Francoise Hollande a wani Otel bayan kammala cin abinci.

shugabannin biyu, sun kuma bayyana fatarsu na ganin Amurka karkashin jagorancin shugaba mai ci Donald TrumpĀ  ta sauya matsayarta kan yarjejeniyar ta Paris don tafiya tare da sauran kasashe.

A baya-bayan nan ne dai shugaba Trump na Amurka ya sanar da janyewar kasarsa daga yarjejeniyar bayan tun farko kasar ta amince da batun karkashin jagorancin Barrack Obama.