Isa ga babban shafi
Faransa

ISIS ta dauki alhakin kaddamar da farmaki a Faransa

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaddamar da harin bindiga tare da garkuwa da mutane a wani katafaren Kanti da ke Kudancin Faransa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku.

Jami'an tsaro sun hallaka maharin da ya yi garkuwa da mutane a wani kanti da ke kudancin Faransa
Jami'an tsaro sun hallaka maharin da ya yi garkuwa da mutane a wani kanti da ke kudancin Faransa REUTERS/Regis Duvignau
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta kafar yada labaranta na Amaq, kungiyar ISIS ta ce, sojanta ya kai harin ne a Trebes don amsa kiran da kungiyar ta yi wa mayakanta na kai hare-hare a kasashen da suka hada rundunar yaki da ita.

Ministan cikin gidan Faransa, Gerard Collomb ya ce, tuni jami’an tsaro suka yi nasara kashe maharin dan shekaru 26 da haihuwa kuma mai suna Redouane Lakdim.

Ministan ya kara da cewa, Lakdim sananne ne ga jami’an tsaro kuma mai safarar miyagun kwayoyi ne, amma ba a san shi da ayyukan ta’addanci ba.

Kazalika majiyar tsaro ta bayyana maharin a matsayin dan asalin kasar Morocco duk da cewa Mr. Collomb bai tabbatar da kasarsa ta asali ba.

Wasu shadiun gani da ido na cewa, maharin ya yi ta kabbara a yayin kai farmakin na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.