rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Bakin-haure Tarihin Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kwashe baki sama da dubu a wani sansani da ke Paris

media
Aikin kwashe baki daga sansanin «Millénaire», arewacin Paris, laraba, 30 ga watan mayun 2018 RFI/Simon Rozé

Bakin haure sama da dubu daya ne ‘yan sanda suka yi amfani da karfi domin kwashewa daga wani sansani da ke wajen birnin Paris na Faransa a wannan laraba.


Tun da sanyin safiya ne aka tura dimbin jami’an tsaro domin kwashe bakin daga wannan sansani, yayin da bayanai ke cewa aikin kwashe ‘yan ci ranin ya gudana a cikin tsanaki.

Tuni aka rarraba mutanen a wasu cibiyoyi na masamman guda 24 da aka bude domin karbar su, yayin da nan take jami’an tsaro suka rusa tantuna da sauran rumfunan da aka kafa a sansanin.

Kantomon mulki a birnin Paris Michel Cadot, ya ce a jimilce mutane 1.016 ne aka kwashe ciki har da yara kanana 11. Wannnan ne karo na 36 da gwamnati ke bai wa jami’an tsaro izinin yin amfani da karfi domin kwashe bakin a cikin shekaru 3.