rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun London ta daure ma'aurata saboda kashe 'yar aiki

media
Sabrina Kouider wadda ta kashe 'yar aikinta da duka bayan ita da mai gidanta sun masa ma ta da duka Metropolitan Police/Handout via REUTERS

Wata kotu a birnin London ta yi wa wasu ma’aurata biyu ‘yan asalin Faransa daurin rai-da-rai a gidan yari bayan ta same su da laifin kashe wata matashiya da ke yi musu aikace-aikace na gida.


Bayanai na cewa, Sabrina Kouider da mai gidanta Ouissem Medouni sun kuma yi kokarin kona gawar Sophie Lionnet mai shekaru 21 bayan sun kashe ta a bara.

Mai shigar da kara a kotun ta Old Bailey, Aisling Hosein ta ce, matashiyar ta mutu ne sakamakon fuskantar azabtarwa da gan-gan.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun musanta aikata wannan laifi da kotu ta ce sun aikata.