Isa ga babban shafi
Faransa-Iraqi

Macron zai dauki nauyin mata 100 na kabilar Yazidi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sha alwashin karba tare da daukar nauyin akalla mata 100 ‘yan kabilar Yazidi na kasar Iraqi wadanda suka fuskanci azabtarwa a hannun kungiyar IS cikin shekarar 2014. 

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ganawarsa da Nadia Murad a fadarsa da ke birnin Paris.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ganawarsa da Nadia Murad a fadarsa da ke birnin Paris. Etienne Laurent/Pool/AFP
Talla

Emmanuel Macron wanda ke sanar da wannan mataki jim kadan bayan wata ganawa da Nadia Murad mai fafatukar kawo karshen cin zarafin mata wadda ta gudana a birnin Paris ya ce matan sun fuskanci cin zarafi da kaskanci.

Nadia Murad wadda ta samu lambar yabo ta Nobel game da yakin da take yi na kawo karshen cin zarafin mata, ta na daya daga cikin dubban mata ‘yan kabilar Yazidi da mayakan IS suka tsare tsawon lokaci, kafin ceto su a wani sumame karkashin jagoran mayakan kurdawa da taimakon dakarun hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta.

Shugaban Macron ya bayyana cewa, 20 daga cikin matan za su iso Faransa kafin karshen wannan shekara, yayin da sauran kuma za su kammala zuwa a shekara mai kamawa.

Zalika Macron ya kara da cewa zai marawa Murad baya kan asusun sake gina Asibitoci da Makarantu a yankin Sinjar, da ta kaddamar da zummar karfafawa ‘yan kabilar Yazidi da ke gudun hijira komawa gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.