Isa ga babban shafi
Faransa

Masu bincike na kokarin tanttance kudadden da Macron yayi amfani da su a zaben sa

Masu shigar da karar birnin Paris na kasar Faransa sun kaddamar da soma wani binciken zargi kan shugaban kasar Emmanuel Macron dake cewa ya karbi taimakon wasu makudden kudadde akalla Euro 144.000 da ya gudanar da yakin neman zabensa da su a shekarar da ta gabataKungiyar dake zura ido kan kudadden yakin neman zabe a faransa ce ta bayyana cewa shugaban ya karbi tallafin yakin neman zabensa .

Emmanuel Macron shugaban kasar Faransa
Emmanuel Macron shugaban kasar Faransa Francois Mori/Pool via REUTERS
Talla

Masu shigar da kara a Faransa sun kaddamar da wannan bincike ne don gano hanyoyin da aka bi tareda zuba makuden kudadden a yakin zaben Shugaban kasar .

Wannan mataki na biyo bayan tseguntawa da wata hukuma dake da nauyin sa ido dangane da yadda ake kashe kudadden yakin zabe.

An dai bayyana cewa an zuba wadanan kudadde ne tareda yin amfani da takardun bankuna, dama aike.

Masu bincike na kokarin gano ko masu taimakawa kungiyar basu wucce adadin da aka kayade na euros 7.500.

An soma wannan bincike ne yan makwanni bayan da shugaban gungun yan adawa Jean Luc Melenchon ya amsa wasu tambayoyi daga masu bincike, sai dai Melenchon ya na danganta wannan yunkuri daga ita hukumar zuwa Shugaban kasar da cewa siyasa ake kokarin yi amfani da ita,babu gaskiya cikin binciken.

Melenchon ya diga ayar tambaya da cewa yan sanda za su iya yi dirar mikiya a gidan Shugaban kasar ,ko kuma za su iya sanar da al’uma sunayen mutanen da suka bada wadanan kudadde.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.