rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Diflomasiya China

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU na bincike kan yi wa rumbun sirrikanta kutse

media
Zargin da EU ke yi na cewa an yi mata kutse a shafukan bayanan sirrikanta na Diflomasiyya da ke Intanet ya zo ne a dai dai lokacin da ta ke shirin gudanar da zabenta na ‘yan majalisu a cikin watan Mayun shekara mai zuwa. AFP/Kirill KUDRYAVTSEV

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da gaggauta gudanar da bincike game da kutsen da wasu mutane da ake zargin alakarsu da China suka yi mata, a rumbun ajiyar bayanan sirrikanta na diflomasiya.


Jaridar New York Times ta rawaito cewa, masu kutsen sun yi amfani da makamancin salon da sojin China ke amfani da shi kafin samun nasarar kutsawa cikin hanyoyin sadarwar Kungiyar Kasashen Turai, kutsen da shi ne mafi girma da aka yi wa wata babbar cibiyar kasa da kasa a duniya a baya-bayan nan.

Kutsen ya tona wasu ayyukan diflomasiyar EU a sassan duniya da suka hada da batun tinkarar shugaban Amurka Donald Trump.

Zalika akwai batun ganawar da aka yi tsakanin Trump da Vladimir Putin a birnin Helsinki a cikn watan Yuli. Sai kuma bayanan sirrin da ke nuna yadda shugaban China Xi Jinping ya soki Trump kan matakansa na huldar kasuwanci.

Wannan kutsen ya tunatar da irin wanda shafin Wikileaks ya fallasa a shekarar 2010, kan tarin ayyukan Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, koda yake wanda aka yi wa EU din bai kai girman na Amukan ba.

Tuni manyan jami’an EU suka ce, sun fara gudanar da bincike kan tonon sililin wanda ke zuwa a dai dai lokacin da Kungiyar ta Turai ke cikin shirin ko-ta-kwana kan kaidin ayyukan intanet da ka iya shafar zabenta na ‘yan majalisu a cikin watan Mayun shekara mai zuwa.