Isa ga babban shafi
Birtaniya

'Yan Birtaniya sun bukaci sake zaben raba gardama kan Brexit

Dubban jama’a daga sassan Birtaniya a Yau Asabar, sun yi zanga-zanga a birnin London, inda suke neman a sake gudanar da zaben raba gardama kan zabin ficewar kasar daga cikin kungiyar kasashen Turai EU.

Jagororin masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa akalla 'yan Birtaniya miliyan 1 ne suka gudanar da tattakin nunawa adawa da ficewarsu daga EU.
Jagororin masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa akalla 'yan Birtaniya miliyan 1 ne suka gudanar da tattakin nunawa adawa da ficewarsu daga EU. AFP/Niklas HALLE'N
Talla

Zangar-zangar na zuwa ne bayanda a tsakiyar mako, shugabannin EU suka amsa bukatar Fira Ministar Birtaniya Theresa, ta neman kara wa’adin lokacin ficewar kasar daga cikinsu, ficewar da a baya aka tsara za ta kammala a ranar 29 ga watan Maris da muke ciki.

Har yanzu dai Fira Minista May na bukatar goyon bayan ‘yan majalisunta, wajen amincewa da yarjejeniyar Brexit da ta cimma da shugabannin EU, wadda suka yi watsi da ita sau 2 a baya.

Muddin kuma a wannan karon ‘yan majalisar suka sake kin amincewa da yarjejeniyar, hakan na nufin tilas Birtaniya ta gaggauta tsara ficewa daga EU ba tare da yarjejeniya ba a ranar 12 ga watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.