rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Bakin-haure Mexico Honduras Guatemala

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya janye tallafin da Amurka ke baiwa wasu kasashe 3

media
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Amurka Donald Trump, ya janye tallafin da yake baiwa kasashen, El Salvador, Guatemala da Honduras, bayan da ya zargi kasashen da turawa Amurka ‘yan ci rani.


Trump ya dauki matakin ne, sa’o’i kalilan, bayan da yayi barazanar rufe kan iyakar Amurka da Mexico duk dai kan batun kwarar bakin hauren cikin Amurkan, matakin da Trump yace zai tabbata muddin kasar ta Mexico ta gaza dakatar da kwarar ‘yan ci ranin ta kan iyakarsu dake yankin kudanci.

A shekarar bara wata tawaga da ta kunshi ‘yan ci rani akalla dubu 7 ta taso daga kasar Honduras da nufin zuwa Amurka, inda tuni suka isa kasar Mexico da ke makwabtaka da ita, abinda shugaba Trump ya bayyana shi a matsayin al’amarin da aka shirya shi da gangan.