Isa ga babban shafi
Birtaniya

An fara takarar maye gurbin Firaministar Birtaniya

An fara fafutukar takarar maye gurbin Firaministar Birtaniya da ta yi murabus Theresa May, inda masu fatan gaje kujerarta suka yi alkawarin cimma nasara a bangaren da ta gaza.

Firaministar Birtaniya Theresa May za ta sauka daga kujerarta a  ranar 7 ga  watan Yuni
Firaministar Birtaniya Theresa May za ta sauka daga kujerarta a ranar 7 ga watan Yuni REUTERS/Susana Vera
Talla

Uwargida May ta sanar da murabus dinta bayan ta gaza cimma nasarar fitar da kasar daga gungun kasashen Turai.

Sai dai ‘yan takarar da ke son darewa kujerarta sun ce, za su fitar da kasar daga Kungiyar Tarayya Turai duk runtsi kuwa.

Tsohon Ministan Harkokin Wajen Kasar, Boris Johnson da ke cikin ‘yan takarar ya ce, za su fitar da Birtaniya daga Turai a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa ko da yarjejeniya ko babu yarjejeniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.