Isa ga babban shafi
Tarayyar turai

Majalisar Tarayyar Turai na zaman neman jagora

Yau Alhamis Majalisar Tarayyar Turai za ta yi zama na musamman domin fara aikin zaben wanda zai gaji shugaban majalisar wato Jean-Claude Juncker da ke daf da kawo karshen wa’adin aikinsa.

'Yan majalisar Tarayyar Turai
'Yan majalisar Tarayyar Turai FREDERICK FLORIN / AFP
Talla

Yanzu haka dai akwai ‘yan takara hudu da ke neman wannan matsayi, wato Manfred Weber dan kasar Jamus, sai Michel Barnier daga Faransa, Frans Timmermans daga Holland sai kuma Margrethe Vestager ‘yar kasar Danemark.

Saura mukaman da ake neman cike gurbinsu har da shugaban Majalisar DokokinTurai,wacce za ta yi zaman ta na farko ranar 2 ga watanYuli, da kuma mukamin jagoran manufofin kasashen waje na Tarayyar.

Shugabannin kasashen Turai suna ta kokarin ganin an gudanar da zaben ta inda za a samu daidaito tsakanin maza da mata, gabas da yamma, damanya da kananan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.