Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta karfafa dakarunta a Afrika

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa yayin ziyarar da yanzu haka ya ke yi a Ivory Coast don gudanar da bukukuwan Kirsimetio tare da dakarunsa da ke yaki a Afrika, ya jaddada aniyar kasar na kara yawan dakaru da nufin kammala murkushe ayyukan ta’addanci a kasashen nahiyar.

Shugaba Emmanuel Macron a tsakiyar dakarun Faransa da ke Ivory coast.
Shugaba Emmanuel Macron a tsakiyar dakarun Faransa da ke Ivory coast. Ludovic MARIN / AFP
Talla

Tuni dai shugaba Macron ya gana tare da cin abincin dare da dakarun Faransar dubu guda da ke sansanin Sojin birnin Abidjan.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Macron ya bayyana cewa za su sauya salon yakin da suke da ta’addanci musamman a kasashen yankin Sahel 4.

Ziyarar ta Macron dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan zanga-zangar kin jinin Sojin Faransar da ta rika gudana a Nijar guda cikin kasashen da Faransar ta girke dakaru da sunan yaki da ta'addanci.

Zangar zangar dai ta faru ne biyo bayan kisan Sojin Nijar 71 da mayakan 'yan ta'adda suka yi wanda ya harzuka al'ummar kasar.

Kafin yanzu dai shugaba Macron ya baiwa kasashen 4 da suka kunshi Nijar, Mali Chadi da kuma Burkina Faso zabin ci gaba da kasancewar dakarun nasa a kasashensu a akasin haka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.