rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Seria A Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Totti na Roma ya yi ritaya

media
Francesco Totti ya yi ritaya a Roma Reuters / Stefano Rellandini

Francesco Totti na Italiya ya yi ritaya a jiya a wasan da Roma ta doke Genoa ci 3 da 2 a Seria A, bayan shafe shekaru 25 yana buga kwallo a kungiyar Roma.


Roma da magoya bayanta sun karrama kaftin din kungiyar a wasan shin a karshe.

Totti mai shekaru 40 ya shafe kuri’arsa yana takawa Roma kwallo inda ya jefa kwallaye 307 a raga a wasanni 786 da ya bugawa kungiyar.

Totti ne dai na uku cikin jerin ‘yan wasan da suka fi haskawa a gasar Seria A ta Italia bayan Polo Maldini da gwalkifan Juventus Gainluigi Buffon.