Isa ga babban shafi
wasanni

Liverpool na jin kamshin kofin firimiyar Ingila

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool ta casa Chelsea ta ci 2-0, abinda ya ba ta damar ci gaba da zama a teburin gasar firimiyar Ingila da maki 85, yayinda Manchester City da ke matsayi na biyu ke da mai 83.

Mohamed Salah na Liverpool
Mohamed Salah na Liverpool AFP/Oli SCARFF
Talla

Sadio Mane da Mohamed Salah ne suka ci wa Liverpool kwallayen biyu.

Kocin Liverpool, Jurgen Kloop ya jinjina wa Salah, yana mai bayyana shi a matsayin jigon cikar burin kungiyar na ganin ta lashe kofin a karon farko cikin shekaru 29.

Kazalika kocin ya yaba wa Salah game da kwallo ta biyu da ya jefa a ragar Chelsea, kwallon da ya ce, ta matukar kayatar da shi.

Ita ma Manchester City ta samu nasarar doke Crystal Palace da ci 3-1 a wasansu na ranar Lahadi.

Yanzu haka wasanni biyar suka rage wa Manchester City, Liverpool kuwa, nada sauran wasanni hudu. Kowacce daga cikin kungiyoyin biyu na fatan ganin ita za ta lashe kofin a bana.

Sai dai akwai wasanni masu zafi a gaban Manchester City da suka hada da haduwarta da Manchester United da Tottenham, kungiyoyin da ke da karsashi matuka, sabanin Liverpool da za ta kara da Cardiff da Huddersfiled da Newcastle da kuma Wolves.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.