Isa ga babban shafi
Wasanni

Za a gudanar da gasar Afrika a Yuni da Yuli

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika, CAF ta tabbatar cewa, za a gudanar da gasar cin kofin nahiyar ta shekarar 2019 a cikin watannin Yuni da Yuli.

Gasar cin kofin Afrika, ita ce mafi girma a nahiyar
Gasar cin kofin Afrika, ita ce mafi girma a nahiyar GABRIEL BOUYS / AFP
Talla

Gabanin wannan matakin dai, ana gudanar da gasar ce mafi girma a Afrika a watannin Janairu da Fabarairu, abin da ke haddasa sabani tsakanin ‘yan wasan nahiyar da kuma kungiyoyinsu na kasashen Turai.

Domin kuwa tilas ne kungiyoyin na Turai su saki ‘yan wasan a tsakiyar kakar wasanni, kuma hakan na ci mu su tuwo a kwarya.

Kazalika kasashen Afrika 24 ne za su fafata a gasar, wadda za a gudanar a Kamaru a shekarar 2019 a maimakon kasashe 16 da aka saba gani tun daga shekarar 1996.

Sannan kuma za a ci gaba da gasar duk bayan shekaru biyu-biyu.

Kwamitin zartaswar hukumar CAF ya rattaba hannu don amincewa da sauye-sauyen da aka kawo a gasar a wani taro da aka gudanar a birnin Rabat na Morocco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.