Isa ga babban shafi
Kenya

'Yan Sanda sun kashe masu zanga-zanga a Kenya

Jami’an ‘yan sandan Kenya sun kashe mutane 11 a kokarinsu na murkushe masu zanga-zangar adawa da sake zaben Uhuru Kenyatta a matsayin shugaban kasa.

Jami'an 'yan sandan Kenya sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da sake zaben Uhuru Kenyatta a matsayin shugaban kasa
Jami'an 'yan sandan Kenya sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da sake zaben Uhuru Kenyatta a matsayin shugaban kasa REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Rahotanni sun ce,’yan sandan sun kuma yi amfani da barkonon tsohuwa a birnin Kisumu, in da aka fi samun tashin hankali a zaben 2007 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 1 da 200 a duk fadin kasar.

Babbar tawagar kasar da ta sanya ido a zaben ta goyi bayan sakamakon da aka fitar wanda ya nuna cewa, Kenyatta ya samu kusan kashi 55 na kuri’un da aka kada.

Tawagar Elog mai kunshe da mambobi dubu 8 da 300 ta ce, sakamakon zaben ya yi daidai da abin da ta tattara a bangarenta.

Shugabar tawagar, Regina Opondo ta ce, ba su gano wani magudi da aka tafka da gan-gan a zaben ba.

Sai din Raila Odinga da ya kasance babban dan adawar Kenyatta a zaben, ya yi watsi da sakamakon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.