Isa ga babban shafi
Kenya

Ana zaman fargaba a Kenya

Hukumar zaben Kenya ta ce ta na sa ran kamala tattara sakamakon zaben shugaban kasar daya gudana a gobe Juma'a, yayinda ake ci gaba da zaman fargaba baya da Raila Odinga ya yi watsi da sakamakon wucin gadin da ya nuna shugaba Uhuru Kenyatta na kan gaba da yawan kuri'u.

dukkanin bangarorin adawar biyu Uhuru Kenyatta da Raila Odinga sun yi tsayuwar dakan ganin sun samu nasara a Zaben wanda za a fitar da sakamakonsa a gobe Juma'a
dukkanin bangarorin adawar biyu Uhuru Kenyatta da Raila Odinga sun yi tsayuwar dakan ganin sun samu nasara a Zaben wanda za a fitar da sakamakonsa a gobe Juma'a Reuters
Talla

Gamayyar ‘yan adawa sun kira taron manema labarai a yau Alhami inda suka bukaci hukumar zaben Kenya ta bayyana dan takararasu Raila Odinga a mastayin wanda ya lashe zaben kasar,

‘Yan adawar sun ce sakamakon da suka samu daga majiya mai tushe a hukumar zaben, ya zama wajibi hukumar zaben ta sanar da Raila Odinga a matsayin wanda ya yi nasara.

Tuni dai Masu sanya ido kan zabe na kasashen waje da suka hada da na Tarayyar Afrika da na renon ingila da Amurka da kuma Tarayyar Turai suka yaba da sahihancin zaben na Kenya.

Dama dai an jima ana fargabar abin da ka iya faruwa tun kafin zuwan zaben na Kenya mai cike da sarkakiya, ganin yadda bangarorin biyu su ka kai makura wajen ganin sun samu nasara, duk da cewa Shugaba Raila Odinga ya alkawarta mika mulki matukar ya tabbata ya sha kaye a Zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.