Isa ga babban shafi
Kenya

Zan mutunta sakamakon zabe- Kenyatta

A yayin da al’ummar Kenya ke kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa a yau Talata, shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya ce, zai mutunta sakamakon zaben, yayin da ake fargabar tashin hankali da ka iya barkewa bayan sanar da sakamakon.

Shugaba Uhuru Kenyatta da abokin hamayyarsa Raila Odinga a Kenya.
Shugaba Uhuru Kenyatta da abokin hamayyarsa Raila Odinga a Kenya. REUTERS/Thomas Mukoya/Baz Ratner
Talla

Shugaba Uhuru Kenyatta da ke fafatawa da tsohon abokin hamayyarsa Raila Odinga ya bukaci bangaren ‘yan adawa da ya mutunta sakamakon zabe kamar yadda shi ma ya dauki alkawari.

Gidan Rediyon Kenya ya rawaito cewa, an samu karamar hatsaniya a kudancin kasar bayan bude rumfunan zabe a sanyin safiyar yau, amma babu wanda aka tabbatar da mutuwarsa.

Idan dai ba a manta ba, an kashe wani babban jami’i a hukumar zaben kasar a yayin da ake dab da kammala yakin neman zabe, yayin da wasu ke zargin cewa, akwai yiwuwar tafka magudi a zaben na yau.

Kimanin mutane dubu 1 da 100 ne suka mutu a shekarar 2007 bayan an samu tashin hankali a zaben kasar, lamarin da kuma ya raba mutane dubu 600 da gidajensu.

Sai dai a wannan karo, masu sanya ido a zaben sun bayyana cewa, manyan ‘yan takarar sun kiyaye harsunansu don kauce wa furta kalaman da ka iya haddasa fitina a kasar.

A karo na biyu kenan da Uhuru Kenyatta ke neman kujerar mulkin kasar, in da ya ke fafatawa da ‘yan takara shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.