Isa ga babban shafi
Kenya

Mutanen Kenya na yin kaura saboda fargabar zabe

Al’ummar birnin Nairobi na Kenya na ci gaba da shirye-shiryen kaurace wa birnin don neman mafaka a yankunan bayan-gari a dai-dai lokacin da ya rage kasa da kwana guda a fara kada kuri’a a  babban zaben kasar.

Kayayyakin zaben shugabancin kasa a Kenya
Kayayyakin zaben shugabancin kasa a Kenya Reuters/Baz Ratner
Talla

Za a fafata ne tsakanin shugaba mai ci Uhuru Kenyatta da kuma abokin adawarsa Raila Odinga a zaben na gobe mai cike da kalubale ganin yadda kowanne bangare ke fatan samun nasara akan abokin karawarsa.

A baya-bayan nan ne dai adadin masu fice wa daga birnin na Nairobi ya karu, sakamakon fargabar da wasu ke yi na maimaituwar abin da ya faru a shekarar 2007, in da sama da mutune dubu 1,100 suka rasa rayukansu, yayin da da dama suka kaurace wa gidajensu.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaba Uhuru Kenyatta ke tsayawa takara tun bayan darewarsa kan karagar mulki a shekarar 2013, yayin da abokin adawarsa Raila Odinga ya sha kaye har sau biyu a takarar shugabancin kasar a shekarar 2007 da kuma 2013.

Duk da cewa jami’an tsaro na yin iya kokari wajen ganin mutane ba su razana da zaben ba, amma mutanen yanzu haka na neman hanyoyin ficewa daga birnin don tsira da lafiyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.