Isa ga babban shafi
Kenya

An bude rumfunar zabe a Kenya

A wannan talatar 'yan kasar Kenya sama da miliyan 19 ke shiga zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisu da za’ayi a fadin kasar, zaben da tuni ya jefa tsoro da shakku kan yadda zai gudana.

Al'ummar Kenya sun fito kada kuri'un su
Al'ummar Kenya sun fito kada kuri'un su Reuters/Thomas Mukoya
Talla

Shugaba Uhuru Kenyatta na fafatawa da tsohon abokin hamayyar sa Raila Odinga, wanda ke takara a karo na hudu.

Rahotanni sun ce 'yan kasar da dama na fargabar tashin hankali lura da irin matsalar da aka samu a shekarun baya wanda ya yi sanadiyar kashe mutane sama da 1,000 a shekarar 2007.

Kafin zaben na yau an samu tashe-tashen hankalu da ma rasa rayuka, cikin su harda wani babban jami’in hukumar zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.