Yan adawar kenya sun yi watsi da sakamakon zabe
Sakamakon farko dake fitowa daga kasar Kenya na nuna cewar shugaba Uhuru Kenyatta ke kan gaba da kashi 55, yayin da Raila Odinga ke da kashi 44 daga cikin kuri’u miliyan 11 da aka kirga.Hadin kan Jam’iyyun adawar kasar Kenya dake goyan bayan Raila Odinga sun ki amincewa da sakamakon farko wanda ya nuna cewar shugaba Uhuru Kenyatta ya kama hanyar rike kujerar shugabancin kasar.
Wallafawa ranar:
Dan takara Raila Odinga yace hukumar zabe bata bada takardun shaidar dake nuna cewar Kenyatta ne ke kan gaba ba da kuri’un da suka zarce nasa ba, inda yace sakamakon na tattare da kura kurai.
Odinga yace wannan ya sasu fargaba lokacin da aka bada sanarwar kisan gillar da aka yiwa Chris Msando, jami’in kula da sashen tattara sakamakon zaben ta hanyar komputa.
Rahotanni dai sun ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali a akasarin fadin kasar, kuma yanzu haka hankula sun koma kan hukumar zaben mai zaman kan ta domin bada sakamako.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu