Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mnangagwa na dab da isa Zimbabwe don karbar jagoranci

A wannan Laraba ake dakon isowar mataimakin shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da Robert Mugabe ya kora, in da ya fice daga kasar sama da makwanni biyu da suka shude.

Emmerson Mnangagwa na shirin shan rantsuwar shugabanci rikon kwaryar Zimbabwe a yau Laraba
Emmerson Mnangagwa na shirin shan rantsuwar shugabanci rikon kwaryar Zimbabwe a yau Laraba REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Daya daga cikin masu taimaka wa Mnangagwa, Larry Mavhima ya shaida wa Kamfain Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, jim kadan da isowarsa kasar, Mnangagwa zai yi jawabi ga manema labarai a takaice.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Jam’iyyar ZANU-PF mai mulki ta ayyana Mnangagwa a matsayin shugabanta don maye gurbin Mugabe.

Ana saran rantsar da Mnangagwa a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya bayan Mugabe ya mika takardar murabus dinsa ga Majalisar Dokokin kasar a yammacin jiya Talata.

Sojin Zimbabwe sun taka muhimmiyar rawa wajen murabus din Mugabe wanda ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 37, yayin da al’ummar kasar ke ci gaba da murnar kawo karshe mulkin Mugabe mai shekaru 93.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.