rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Robert Mugabe

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mugabe zai gurfana gaban Majalisar kasar kan bacewar dala biliyan 15

media
Majalisar ta ce dole ne Mugabe ya gurfana gabanta don yin jawabi kan bacewar kudin la'akari da cewa a lokacin mulkinsa ne suka bace. Phill Magakoe / AFP

Kwamitin da Majalisar kasar Zimbabwe ta kafa domin gudanar da bincike kan zargin asarar da kasar ta tafka wajen cinikin lu’u lu’u ya sha alwashin gayyatar tsohon shugaban kasar Robert Mugabe don bada shaida a gaban ta.


Majalisar ta ce za ta bukaci Mugabe ya yi musu bayani kan bacewar Dala biliyan 15 a shekarar 2016 daga kudaden shigar da ake samu wajen hakar ma’adinin saboda cin hanci da kuma kaucewa biyan haraji.

Temba Mliswa, shugaban kwamitin binciken ya ce suna bukatar Mugabe ne a matsayinsa na wanda ya ke kan karagal mulki lokacin bacewar kudin.