rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sabon kawance na yan adawa a Nijar

media
Ibrahim Yakouba,Shugaban jam'iyyar MPN KISHIN KASA a Nijar rfi hausa

A Jamhuriyar Nijar, tsohon Ministan harakokin wajen kasar Ibrahim Yakouba da shugaban Nijar Mahamadou Issifou ya salama a watan Afrilu ya kafa sabuwar kawance ta biyar da ta hada jam’iyyoyin adawa, kungiyoyin farraren hula da aka yiwa sunan Front Patriotique domin kare demokkuradiya a kasar ta Nijar.


An dai gudanar da wannan gaggarumin taro a dakin taro na palais de Congres na birnin Yameh,inda Ibrahim Yakouba shugaban wannan gungun ya bayyana cewa gwamnatin Mahamadou Issifou ba ta cika alkawura da ta dau a baya ba, sai dai wani abin lura shine ga baki dayan su manyan yan siyasa bangaren adawa ba su halarci wannan zaman taro ba.