Za a hukunta 'yan sandan da suka kashe dan Najeriya
Yau ake sa ran hukumomin Afrika ta Kudu za su gurfanar da jami’an ‘yan sandansu guda 8 da ake tuhuma da laifin kashe wani dan Najeriya, Ibrahim Badmus, bayan azabtar da shi a watan Oktoban bara.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A karshen makon da ya gabata ne wata tawagar ‘yan sanda ta musamman ta cafke wadannan jami’an da ake zargi da kisan Badmus da suka hada da Ms. Catherine Tenteza, Ms. Gerhard Der-Walt, Mr. Nkosinathi Ngwenya, Mr. Aaron Arends, Mr. Nomkhosi Khoza, Mr. Emmanuel Ngwane, Mr. Msebenzi Mkhuma da kuma Mr. Joseph Mamasela
Jakadan Najeriya a kasar Godwin Adama ya ce matakin zai karfafa gwuiwa ga ‘yan kasashen waje da ke zama a Afrika ta Kudu da ke zargin jami’an tsaro da cin zarafinsu.
‘Yan Najeriya sun nuna bacin ransu matuka da kisan Badmus, yayin da a farko ‘yan sandan suka ce, wasu masu fataucin miyagun kwayoyi ne suka kashe shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu