Isa ga babban shafi
Kamaru

An jinkirta sakin 'yan awaren da gwamnatin Kamaru ta yiwa afuwa

An samu jinkiri wajen sakin fursunoni 289 da gwamnatin Kamaru ke tsare da su bisa samunsu da laifi a rikicin ‘yan awaren kasar masu neman kafa kasar Ambazonia.

Daya daga cikin yankunan da rikicin 'yan aware ya lalata a kasar Kamaru.
Daya daga cikin yankunan da rikicin 'yan aware ya lalata a kasar Kamaru. AFP/MARCO LONGARI
Talla

Jinkirta sakin fursunonin ya zo ne kwana guda bayan da shugaban Kamaru Paul Biya ya sanar da yi musu afuwa a ranar Alhamis.

A wannan Juma’a ce kuma wasu kotunan kasar guda shida suka bada umarnin sakin fursunonin, to sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito kafar rediyon kasar, na cewa an samu jinkirin ne a dalilin wasu ka’idoji na gudanarwa da ba’a kammala cikawa ba.

Zuwa yanzu dai akalla fararen hula 500 da jami’an tsaro 200 ne suka hallaka sakamakon rikicin ‘yan awaren a arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin Kamaru, tun bayan da masu fafutukar ballewa daga kasar suka dauki makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.