Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru ta kaddamar da shirin kwance damarar masu tada kayar baya

Gwamnatin Kamaru ta kaddamar da wani sabon tsari na kwance damarar mayaka masu tada kayar baya a yankunan kasar masu fama da rikici, da suka hada da yankunan arewaci da na ‘yan aware.

Wasu sojin Kamaru dake cikin rundunar dakarun hadin gwiwar kasashe masu fama da rikicin Boko Haram a Fotokol. 19/2/2015.
Wasu sojin Kamaru dake cikin rundunar dakarun hadin gwiwar kasashe masu fama da rikicin Boko Haram a Fotokol. 19/2/2015. Edwin Kindzeka Moki/AP/SIPA
Talla

Matakin da fadar shugaban Kamaru ta sanar, ta ce gwamnati ta kafa kwamitin da aka dorawa nauyin tafiyar da wannan jan aiki na kwance dammarar mayakan tare da sama masu hanyoyin sake dawowa tsakanin al’umma ba tareda tsangwama ba.

Kwamitin zai gudanar da gagarumin aikin ne a karkashin wani tsari da aka sanyawa sunan CNDDR, karkashin jagorancin Frammistan kasar Philimon Yan, shugaban kwamitin.

Kwamitin wanda hedikwatarsa za ta kasance a birnin Yaoundé, zai kafa cibiyoyinsa a garuruwan Bamenda da Buea wadanda su ne manyan biranen yankunan ‘yan kasar marasa rinjaye masu amfani da turancin Ingilishi, dake neman kafa kasar Ambazonia.

Daga bangaren arewacin kasar mai fama da hare-haren Boko Haram kuwa, kwamitin kwance damarar ‘yan tada kayar bayan, zai kafa cibiyarsa ce a garin Mora.

Kaddamar da shirin kwance damarar mayakan masu tada kayar baya, ya zo ne bayan ganawar da shugabannin kasashen Najeriya, Nijar Kamaru da Chadi suka yi a N’Djamena ranar Alhamis, domin tattaunawa kan yadda za’a shawo kan karuwar hare-haren mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi da ya shafi iyakokin kasashen hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.