Isa ga babban shafi
Gabon

Shugaban Gabon ya koma gida

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba ya koma gida bayan kwashe watanni yana jinya a kasashen waje sakamakon bugun zuciyar da ya samu lokacin da yake halartar wani taro a Saudi Arabia.

Rantsar da sabin Ministocin Gabon a fadar Shugaban kasar dake Libreville
Rantsar da sabin Ministocin Gabon a fadar Shugaban kasar dake Libreville Gabon Presidency
Talla

A jiya shugaban ya jagoranci bikin rantsar da sabbin ministocin gwamnatin sa 38, matakin da a karon farko ya baiwa yan kasar damar ganawa da shi.

Kakakin gwamnati, Nanette Longa-Makinda ya bayyana cewar abin farin ciki ne sake ganin shugaban, yayin da wani minista yace zai dauki dogon lokaci kafin shugaban ya gama murmurewa.

Ana sa ran Ali Bongo ya sake komawa kasar Morocco wajen ci gaba da karbar magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.