Isa ga babban shafi
Mali

Mahara sun hallaka Fulani sama da 100 a Mali

Rahotanni daga Mali sun ce adadin Fulani makiyaya da wasu mahara suka hallaka ya karu daga 60 zuwa sama da mutum 100.

Wasu Fulani makiyaya da ke kudanci yankin Douentza, a kasar Mali.
Wasu Fulani makiyaya da ke kudanci yankin Douentza, a kasar Mali. Human Rights Watch
Talla

Tun da fari dai, magajin garin Bankass da ke tsakiyar yankin Mali, Moulaye Guindo, ne ya soma bayyana rahoton harin kan Fulanin makiyaya a kauyen Ogossogou-Puel.

Adadin mamatan ya karu ne zuwa 115, bayan da hadin gwiwar jami’an tsaro da sauran jama’ar kauyen suka kammala tantance wadanda harin ya rutsa da su, inda aka gano gawarwakin mutanen da suka bace.

‘Yan bindigar da ake kyautata zaton cewa maharba ne daga kabilar Donzo, sun kai mummunan farmakin ne da misalin karfe 4 na asubahin yau Asabar.

Yankin Tsakiya Mali a baya bayan nan yayi kaurin suna wajen fuskantar matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren mayaka masu da’awar Jihadi da kuma rikicin kabilanci tsakanin kabilun Dogon, Bambara da kuma Fulani. Sai dai a mafi akasarin lokuta an fi kaiwa Fulani makiyaya farmaki, inda ake hallaka da dama daga cikinsu.

Ko a watan Maris na shekarar 2018, dubban Fulani ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Bamako na kasar Mali, domin nuna bacin ransu dangane da yadda ake kai wa kabilar hare-hare bisa zargin cewa ‘yan ta’adda ne.

Fulani, sun fara fuskantar matsala a kasar ta Mali ne sakamakon bayyanar wata kungiya ta ‘yan ta’adda a garin Macina, garin da ke matsayin babbar cibiya ga kabilar ta Fulani a kasar.

Kungiyar ‘’Andal Pulaako Mali’’ wadda ta bukaci a gudanar da zanga-zangar a jiya alhamis, ta yi zargin cewa an kashe Fulani akalla 25, raunata wasu da kuma kona gidajensu duk da cewa ba su da alaka da wata kungiya ta ta’addanci.

To sai dai yayin da wasu ke zargin su da ta’addanci, su ma kansu ‘yan kabilar ta Fulani ba su tsira daga hare-haren da kungiyoyin ta’addanci ke kai wa a sassa daban daban na kasar ta Mali ba, lamarin da ya sa kungiyar ta Andal Pulaako Mali ta bukaci mahukuntan kasar da su bai wa Fulanin kariya ta tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.