rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bouteflika zai yi murabus a cikin watan Afrilu

media
Shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika. Reuters

Fadar gwamnatin Algeria ta ce shugaban kasar AbdelAziz Bouteflika zai yi murabus kafin ranar 28 ga watan Afrilu, lokacin da wa’adinsa zai kare.


Matakin amincewa da yin murabus din Bouteflika, ya zo ne bayan da manyan jam’iyyun siyasar kasar cikin har da tasa, suka goyi bayan dubban ‘yan kasar da ke zanga-zangar neman tilasta masa sauka daga mulki.

Cikin sanarwar da ta fitar a yau Litinin, fadar Gwamnatin ta Algeria ta ce shugaba Bouteflika mai shekaru 82 zai sauka ne bayan daukar wasu muhimman matakai, wadanda ba a bayyana ba.

Matsin lambar tilastawa Bouteflika yin murabus ya soma ne bayanda shugaban ya bayyana aniyar neman wa’adi na 5 a babban zaben kasar da a baya aka tsara zai gudana a ranar 18 ga watan Afrilu.

Bayan zafafar zanga-zangar dubban ‘yan Algeria, Bouteflika ya janye aniyarsa ta neman tazarce, amma da sharadin dage zabukan kasar zuwa wani lokaci da bai bayyana ba.

Matakin shugaban na Algeria ya sake tunzara masu zanga-zangar wadda dubban dalibai da malamansu da kuma manyan lauyoyi suka shiga.