rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Tattalin Arziki Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugabannin kasashen Afirka na halartar taron AU a Yamai

media
Wani bangaren harabar zauren taron kungiyar kasashen Afirka AU a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar. ISSOUF SANOGO / AFP

Yau lahadi ake fara taron shugabannin kasashen Afirka a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, taron da zai tattauna dangane da batutuwan da suka shafi nahiyar, tare da bikin kaddamar da yarjejeniyar kasuwancin ba-daya tsakanin kasashen.


Kafin tsakiyar daren da ya gabata, akwai shugabannin kasashe kusan 20 da suka isa a birnin na Yamai domin halartar taron na tsakiyar shekara, wanda bisa ga al’ada kan tattauna tare da daukar matakai da dama da suka shafi Afrika.

Sha’anin tsaro, siyasa da kuma tattalin arziki, a dunkule su ne muhimman batutuwan da shugabannin za su tattauna a kai, to sai dai kaddamar da yarjejeniyar kasuwanci da ke nufin cire shinge a tsakanin kasashen Afirka, shi ne jigon taron da ake farawa a yau.

Ita dai wannan yarjejeniya kamar yadda shugabanni da masana a nahiyar ke cewa, za ta sa kasuwanci ya bunkasa a tsakanin kasashen daga kashi 15% a halin yanzu zuwa akalla kashi 45% a cikin gajeren lokaci, yayin da a hannu daya nahiyar za ta rika yin magana da murya daya a duk wasu batutuwan da suka shafi tattalin arziki a duniya.

Akwai dai baki sama da dubu 4 da ke halartar wannan taro, da suka hada da shugabannin kasashe da na gwamnatoci daga Afirka, sai kuma wakilai daga kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai, kungiyoyin fararen hula, ‘yan kasuwa da dai sauransu.