Isa ga babban shafi
AU-Nijar

AU ta yi haramar taronta a Jamhuriyar Nijar

Tawagogi daga kasashen Afirka sun fara isa a jamhuriyar Nijar, domin halartar taron tsakiyar shekara na kungiyar Tarayyar Afirka, wanda zai mayar da hankali kan yarjejeniyar kasuwaci ta bai-daya a tsakanin kasashen nahiyar.

Wasu shugabannin kasashen nahiyar Afrika
Wasu shugabannin kasashen nahiyar Afrika Reuters
Talla

Taron wanda ake saran ya samu halarta akalla shugabannin da wakilan kasashen nahiyar 52 daga cikin 55 da suka amince da rattaba hannu kan yarjejeniyar kasuwancin ta bai daya, zai mayar da hankali kan yadda sabuwar yarjejeniyar za ta fara aiki.

Kungiyar ta EU dai na da fatan samar da tsayayyiyar kasuwar Nahiyar ta yadda al'ummar kasashen na Afrika Biliyan 1 da miliyan dari 2 za su amfana da kasuwancin akalla Dala tiriliyan 2 da biliyan 5.

Cikin watan Maris na bara ne dai kasashen suka amince da zagayen farko na yarjejeniyar, yayin taronsu a birnin Kigali na Rwanda, ko da dai jigo a yawan al'umma da kuma kasuwancin nahiyar Najeriya ta ki amincewa da sanya hannu a yarjejeniyar.

A ranar 7 ga watan Yulin nan ne ake saran a kammala cimma jituwa kan yarjejeniyar tare da sanya ta a daftari baya ga mayar da ita doka tsakanin kasashen 55.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.