rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mozambique

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masu sanya ido sun tabbatar da sahihancin zaben Mozambique

media
Masu kada kuri'a a zaben Mozambique PATRICK MEINHARDT / AFP

Masu sa ido na kasashen duniya sun bayyana cewar an gudanar da zaben shugaban kasar Mozambique cikin kwanciyar hankali, sai dai sun yi korafi kan yadda aka gudanar da rajistar masu kada kuri’u da baiwa 'Yan adawa damar gudanar da yakin neman zaben su.


Ignacio Sanchez Amor, jagoran masu sa ido daga kasashen Turai ya ce sun gamsu da yadda aka gudanar da zaben, sai dai ya bayyana damuwa kan yadda Jam’iyyar dake mulki ta hana yan adawa samun damar gudanar da yakin neman zaben su yadda ya kamata.

Tsohon shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya bayyana damuwa kan yanayin tsaro da rajistar masu kada kuri’u da kuma tantance masu sa ido, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasar Kenya Kalonzo Musyoka dake jagorancin tawagar kasashe renon Ingila yayi korafi kan zargin wadanda ake amfani da katunan su wajen kada kuri’a.