rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Yemen

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan tawayen Houthi sun yi barazanar kai hari muhimman gurare a Saudiya

media
Mayakan 'yan tawayen Houthi na Yemen REUTERS/Khaled Abdullah/File Photo

Shugaban 'Yan Tawayen Houthi da ke Yemen, Abdulmalik al-Huthi ya yi gargadin cewar suna iya kai hari muhimman wuraran dake Saudi Arabia da Daular Larabawa dake jagorancin yaki akan su yanzu haka.


Al Huthi ya ce 'yan Tawayen a shirye su ke su ci gaba da kai hare hare kan dakarun kawancen da ke kai musu hari a yakin da aka kwashe shekaru 4 ana fafatawa, kuma makaman su masu linzami na iya kai wa Riyadh da Abu Dhabi da kuma Dubai.

Yayin wata hira da aka yada ta kafar talabijin, shugaban 'Yan Tawayen ya ce a shirye dakarunsu su ke a kasa da kuma bakin daga, kuma a shirye suke su sadaukar da rayukan su.