Isa ga babban shafi
Mali-ECOWAS

Makwabtan Mali sun yi gargadin rufe kan iyaka

Kasashe masu makwabtaka da kasar Mali sun bukaci gwamantin Sojin kasar gaggauta mika mulki ga farar hula kafin ranar Litinin ko kuma a rufe kan iyakokin kasar tare da dakili asusun tallafin da kasar ke samu daga babban bankin kasashen Yammacin Afrika.

Jagoran Juyin mulkin kasar Mali, Kaftin  Amadou Sanogo yana amsa waya tare da tawagar mabiyan shi
Jagoran Juyin mulkin kasar Mali, Kaftin Amadou Sanogo yana amsa waya tare da tawagar mabiyan shi Reuters
Talla

A ranar 22 ga watan Maris ne Sojoji suka kifar da gwamnatin Farar hula ta amadou Toumani Toure bisa zargin gazawar gwamnatinsa wajen yaki da ‘Yan tawaye.

Sanarwar rufe iyakokin kasar ta fito ne daga shugaban ECOWAS Alassane Ouattara shugaban kasar Cote d’Ivoire wadanda aka haramtawa jirginsu sauka birnin Bamako a wata ziyarar da suka shirya kai wa a kasar Mali.

Shugaban gudanarwar ECOWAS, Desire Kadre Ouedraogo yace Sun ba Sojin Mali sa’o’I 72 zuwa ranar Litinin 2 ga watan Afrilu su gaggaunta mika mulki ga farar hula ko kuma Mali ta fuskanci Takunkumi karkashin yarjejeniyar da shugabannin kungiyar suka amince.

Takunkumin dai zai gurgunta tattalin arzikin kasar Mali tare da haramtawa Turawa ci gaba da aikin hako zinari a cikin kasar.

Wannan barazanar wata manuniya ce game da yadda kasashe masu makwabtaka da Mali suke nuna adawarsu akan juyin mulkin da Sojoji suka yi a kasar.

Ana hasashen shugabannin kasashen Cote d’Ivoire da Benin da Burkina Faso da Liberia da Nijar zasu sake shirya kai wata Ziyara zuwa kasar Mali domin tattaunawa da Sojin kasar.

Hambararren Shugaban kasar Mali, Amadou Toumani Toure ya kwashe tsawon shekaru 10 yana shugabancin kasar kuma ya kudurta kawo karshen mulkinsa a zaben da za’a gudanar a watan Afrilu.

A wata Hira da shugaban ya yi da gidan Rediyon Faransa, shugaban ya bayyana cewa yana cikin kasar Mali kuma cikin koshin Lafiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.