Isa ga babban shafi
Mali-ECOWAS

Sojin Mali zasu dawo da kundin tsarin mulki amma ‘Yan tawaye sun karbe Timbuktu

Shugabannin kungiyar yammacin Afrika ta ECOWAS zasu gana game da Mali bayan yin barazanar kargamawa kasar Takunkumi idan har sojin kasar basu dawo da kundin tsarin mulkin ba zuwa yau Litinin. Amma Sojin kasar sun yi alkawalin dawo da kundin tsarin mulkin bayan ‘Yan tawaye sun karbe ikon Timbuktu.

Jagoran Juyin mulkin kasar Mali, Kaftin  Amadou Sanogo a Lokacin da yake ganawa da manema Labarai.
Jagoran Juyin mulkin kasar Mali, Kaftin Amadou Sanogo a Lokacin da yake ganawa da manema Labarai. Reuters/Luc Gnago
Talla

A yau Litinin ne wa’adin da kungiyar ECOWAS ta ba Sojin Mali ya kwao karshe domin komawa Bariki, a dai dai lokacin da ‘Yan tawayen kasar Mali ke kokarin mamaye yankin kudanci.

Amadou Sanogo jagoran juyin mulkin kasar Mali, ya yi alkalin dawo da kundin tsarin mulki kafin gudanar da zabe. Amma har yanzu kungiyar ECOWAS ba tace komi ba game da yunkurin Sojin kasar bayan barazanar rufe iyakokin kasar tare da rufe asusun babban bankin kungiyar dake ba Mali Tallafi.

Shugaban kasar Cote d’Ivoire Allassane Ouattara wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS yace ya zanta da shugaban Sojin Mali domin godiya ga yunkurin dawo da kundin tsarin mulkin kasar.

Sai dai babu wani haske da Ouattara ya bayar game da barazanar takunkumin kasar Mali.

A ranar 22 ga watan Maris ne Sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Amadou Toumani Toure.

A yau Litinin ne shugabannin kasashen ECOWAS zasu gana a Dakar domin tattauna juyin mulkin kasar Mali a lokacin da Macky Sall zai karbi rantsuwar kama aiki a Senegal.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.