Isa ga babban shafi
Kenya

An kori Ministan kula da dabbobi akan rikicin Kenya

Gwamnatin Kasar Kenya, ta kori karamin Ministan kula da dabbobi, Dhadho Godhana, saboda zargin da ake masa na tinzira rikicin kabilancin da ya yi sanadiyar kashe mutane sama da 100, kana kuma aka gurfanar da shi a gaban kotu. Tsohon ministan ya ki amincewa da tuhumar, abinda ya sa mai shari’a, ya bada belinsa, kuma zai sake gurfana a gaban kotun a ranar biyu ga watan gobe. 

Shugaban kasar kenya Mwai Kibaki
Shugaban kasar kenya Mwai Kibaki (Photo : Reuters)
Talla

Jiya ne shugaban kasa Mwai Kibaki, da Firaminista, Raila Odinga, suka sanar da korar ministan daga mukaminsa.
 

Bayyanar Godhana a gaban kotun ta zo ne sa’o’i kadan bayan Kibaki ya bada izinin kama da kuma tuhumar shugabannin da ke ruruta wutar rikicin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 a watan daya gabata.

An dai jibge jami’an tsaro a yankin, a yayin da Kibaki ya saka dokar ta baci daga safe zuwa yamma.

Rikicin wanda ke faruwa tsakanin ‘Yan kabilar Pokomo wadanda manoma ne da ‘Yan kabilar Orma wadanda makiyaya ne ya yi sandiyar mutane da dama a kasar ta Kenya, wacce ta dade bata ga rikici irin wannan ba tun bayan rikicin siyasar da aka yi na bayan zabe.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.