Isa ga babban shafi
Kamaru

Paul Biya ya yi bukin cika shekaru 30 yana saman Mulki a Kamaru

‘Yan sandan Kamaru sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa gungun masu zanga zangar adawa da shugaba Paul Biya wanda ya yi bukin cika shekaru Talatin yana shugabancin kasar.

Wani katon Allon hoton Paul Biya, Shugaban kasar Kamaru
Wani katon Allon hoton Paul Biya, Shugaban kasar Kamaru AFP PHOTO / STR
Talla

Biya mai shekaru 79, a shekarar 2011 ne aka zabe shi wa’adi na Shida bayan ya samu rinjayen kuri’u kashi 78, amma  ‘Yan adawa a lokacin sun yi zargin an tabka magudi.

Daruruwan magoya bayan jam’iyyun adawa ne suka hada gangami a birnin Douala domin adawa da yawan shekarun da shugaban ya kwashe a saman mulki, kafin ‘Yan Sanda su tarwatsa su da harsashe mai fitar da hayaki mai sa hawaye.

Wani dan Majalisa daga bangaren ‘Yan adawa Jean Michel Nintcheu yace sun fito ne suna zanga zangar lumana kafin suka yi kicibis da ‘Yan Sanda wadanda suka abka masu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.