Gambia ta fice daga Kungiyar renon Ingila
Kasar Gambia ta sanar da ficewar ta daga kungiyar kasashe renon Ingila, bayan ta kwashe shekaru 48 a matsayin Mamba. Shugaba Yahya Jammeh, ya bayyana kungiyar a matsayin wani dubaru na mulkin mallaka don ci gaba da jan ragamar yadda ake gudanar da mulki a kasashen Afrika.
Wallafawa ranar:
Shugaban ya dade yana zargin Birtaniya da tallafawa ‘Yan adawar kasarsa, wanda ake zargi yana keta hakkin bil’adama.
Kungiyar Commonwealth ta kunshi kasashe sama da 50 wadanda gwamnatin Birtaniya ta yi wa mulkin Mallaka. Sai dai kuma babu wani cikakken bayani da gwamnatin Gambia ta bayar game da matakin ficewa daga kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu