Isa ga babban shafi
Madagascar

Ana zaben kasar Madagascar zagaye na biyu

Ana gudanar da zaben shugaba kasa a zagaye na biyu a kasar Madagascar, inda ake sa ran hakan zai magance rikicin siyasa da na tattalin arziki da suka addabi kasar da ke tsibiri a kan tekun indiya. Tun da karfe 6 na safiyar yau juma’a agogon kasar, jama’a suka fara layi don kada kuri’a, da suke fatan zaben zai taimaka wajen fidda kasar daga yakin da ta fada tun bayan juyin mulkin da ak yi a shekarar 2009, lamarin daya yi sanadiyyar dakatar da tallafin da kasashen waje ke baiwa kasar.Manyan ‘yan takara biyu ne suke fafatawa a zaben da suka hada da Robinson Jean Loius mai samun goyon bayan tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana da kuma Hery Rajaonarimampianana wanda ke samun goyon bayan shugaban rikon kwaryar kasar Andry Rajoelina.A kokarin su na sasanta rikicin da ya dabaibaye kasar, kasashen duniya sun bukaci Marc Ravalomanana da Andry Rajoelina, kar su yi takarar shugabanci, lamarin da ya sa su goyan bayan ‘yan takarar da ke fafatawa a zabe. 

Wasu masu kada kuri'a a birnin Antananarivo na kasar Madagascar
Wasu masu kada kuri'a a birnin Antananarivo na kasar Madagascar REUTERS/Thomas Mukoya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.