Cutar Ebola ta kashe mutane 208 a Guinea-WHO
Hukumar lafiya ta Duniya WHO, tace adadin mutanen da suka mutu sanadiyar cutar Ebola a kasar Guinea, sun kai 2008, tare da kwatanta cutar a matsayin mafi muni da ta auku tun bulluwarta.
Wallafawa ranar:
Hukumar tace akwai mutane 328 da aka tabbatar da suna dauke da cutar a Guinea cikinsu har da 208 da suka mutu. Cutar kuma yanzu ta yadu zuwa kasar Saliyo da Liberia.
Hukumar WHO tace mutane 79 ne suka kamu da cutar a kasar Saliyo. A kasar Liberia kuma mutane 6 ne aka ruwaito sun mutu.
Likitoci sun ce cutar na yaduwa ne saboda mutane ba su son zuwa Asibiti, suna dogaro da maganin gargajiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu