Isa ga babban shafi
Malawi

An yi wa fursunoni 403 afuwa a Malawi

Shugaban kasar Malawi Peter Mutharika ya yi afuwa ga Fursunoni 403 a yau Assabar a dai dai lokacin da al’ummar kasar ke soma bikin cika shekaru 50 da samun ‘Yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya. A cikin sanarwar da Ma’aikatar cikin gida ta fitar tace lokaci ne da gwamnati ta ga ya dace ta yi afuwa domin bikin samun ‘yancin kai a gobe Lahadi.

Peter Mutharika sabon shugaban kasar Malawi.
Peter Mutharika sabon shugaban kasar Malawi. AFP PHOTO / AMOS GUMULIRA
Talla

A can baya ma Tsohuwar shugabar kasar Joyce Banda ta taba yin afuwa ga fursunoni kusan 400 a lokacin da kasar ke bikin cika shekaru 48 da samun yancin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.