Isa ga babban shafi
Libya-Turai

EU na nazarin tura tawaggar zaman lafiya zuwa kasar Libya

A jiya litanin Kungiyar tarayyar Turai ta bukaci babban jami’in diplomasiyar ta, da yayi nazarin wasu hanyoyin da zasu kai ga tura tawagar neman zaman lafiya a kasar Libiya. Za a tura tawaggar ne idan an kammalar tattaunawar da ake yi, don duba yuwuwar kafa gwamnatin hadin kai dake gudana yanzu haka a kasar Maroko.Yanzu haka dai ana ci gaba da tattaunawa tsakanin majalisun dokokin, da bangarorin da ke rikici da juna a kasar ta Libiya, a wani guri dake kusa da birnin Rabat babban birnin kasar Maroko a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.Ministocin harakokin wajen kungiyar ta tarayyar Turai da suka gudanar da wani zaman taro a jiya a birnin Bruxelles na kasar Belgium, sun ce, da zarar an cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa da kuma tsaro tsakanin tsakanin bangarorin dake gaba da juna a kasar ta Libiya, to kungiyar ta Turai a shirye take ta kara baiwa kasar goyon baya.har ila yau taron ministocin harakokin wajen kasashen Turan, ya bayyana aniyarsa ta tura tawagar dakarun soja ko farar hula, domin agazawa tattaunawar da ake yi karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya da kuma masu fada aji na bangaren adini a kasar.Tawaggar zata taimaka wajen sake maido da tsaro, doka da oda a karkashin ingantaciyar gwamnati hadin kai a Libiya, kasar da yakin basasar tsawon shekaru 4 ya daidaita tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Ma’ammar kaddafi a shekarar 2011.  

Wani dan tawayen kungiyar Fajr a kasar Libya
Wani dan tawayen kungiyar Fajr a kasar Libya AFP PHOTO/MAHMUD TURKIA
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.