Isa ga babban shafi
Libya

Human Rights Watch tace ana amfani da bama bamai masu 'ya 'ya a Libya

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch tayi gargadin cewar an kwashe watanni hudu ana anfani da bama bamai masu ‘ya ‘ya, a yakin da ake tsakanin mayakan dake biyayya ga gwamnatocin dake ikrarin iko da kasar Libya.Wata sanarwar da kungiyar ta fitar a birnin Beirut na kasar Lebanon, ta nuna cewa akwai shaidun dake nuna yadda bangarorin biyu suka yi anfani da bama baman masu ‘ya ‘ya da aka haramta anfani da su a yake yake.Kungiyar tace tattaunawar da tayi da mutanen yankin da aka yi anfani da makamin da kuma hotunan da aka dauka sun tabbatar da yin anfani da su a garin Bin Jawad dake Gabashin kasar ta Libya.Rundunar sojin saman kasar wadda ke biyayya ga gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita, tace ta kai harin sama a yankunan guda biyu da ake zargi an dana irin wadancan bama baman.Sai dai shugaban sojojin kasar, Birgediya Janar Sagr al-Jerouchi ya shaidawa kungiyar cewar su basu da irin wadanan bama baman duk da yake suna ci gaba da kai harin sama yankin.Daraktan kungiyar Human Rights Watch Steve Goose, yace anfani da makamin abin tsoro ne. 

Alamar kungiyar kare hakkin dan Adam ta HUman Right Watch
Alamar kungiyar kare hakkin dan Adam ta HUman Right Watch © Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.