Isa ga babban shafi
Boko Haram

Zamu kafa rundunar kawar da Boko Haram-Boni Yayi

Shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi  ya ce kasashen da ke tunkarar mayakan Boko Haram za su dauki matakan kafa wata runduna, da zata kawar da kungiyar.Boni Ya yi  ya fadi haka, yayin da shugabannin kasashen yankin yammacin Africa ke shirin taro kan lamarin, a gobe Alhamis a birnin Abuja.

Shugaban kasar Bénin, Thomas Boni Yayi a wata ganawa da Shugaban Faransa François Hollande
Shugaban kasar Bénin, Thomas Boni Yayi a wata ganawa da Shugaban Faransa François Hollande AFP PHOTO / POOL / THIBAULT CAMUS
Talla

Dama Kasashen da ke makwabta da Nigeria sun yi ta kiran a yi aiki tare, da kuma kafa rundunar hadin gwiwa don yakar kungiyar, da za a yiwa Shalkwata a N'Djamena, babban birnin kasar Chadi.

Sai dai kuma wannan matakin ya sami tsaiko, ganin yadda mahukuntan Nigeria na wancan lokacin, suka yi ta kaucewa daukar wannan matakin, saboda gudun shigar sojojin kasashen waje zuwa kasar.

Sai dai shugaban kasar ta Benin, Boni Yayi, da ke magana bayan ganawa da Shugaban Faransa Francois Hollande, a birnin Paris, ya ce da gaske sabon shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ke yi, a kokarin kawar da kungiyar ta Boko Haram.

Boni Yayi, ya ce tattaunawar da suka yi da Mr. Hollande ta basu kwarin gwiwar cewa za su iya kawar da wannan jan aiki.

Zuwa yanzu dubub-dubatar mutane ne suka rasa ransu sakamakon rikicin na Boko Haram, yayin da wasu fiye da Miliyo 1 da rabi suka tsere daga gidajensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.