Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane sama da 30 a Zamfara

Rahotanni daga Najeriya na cewa a halin yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 30 sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Chigama da ke cikin karamar hukuamar mulki birnin-Magaji a jihar ta Zamfara.

Taswirar Jahar Zamfara a Najeriya
Taswirar Jahar Zamfara a Najeriya
Talla

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaita shugaban karamar hukumar mulkin ta Birnin-Magaji Muhammad Gusami na cewa maharan sun afkawa kauyen na Chigama da kuma wani kauyen da ke kusa ne a cikin daren ya gabata, inda suka rika harbe jama’a yayin da suka cinna wa wasu wuta.

Yanzu haka dai akwai wasu mutanen da dama da suka shiga jeji sakamakon firgita. Wannan dai ba shi ne karo na farko da ‘yan bindiga ke kai wa garuruwan da ke cikin yankin na Birnin Magaji hari ba inda suke kashe jama’a wasu lokuta tare da wawashe dabbobinsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.